18
1 Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai;
yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.
2 Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta
amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.
3 Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo,
haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.
4 Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye,
amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu.
5 Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri
ko ka hana wa marar laifi adalci.
6 Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa,
bakinsa kuma kan gayyaci dūka.
7 Bakin wawa lalatar da kansa yake yi
leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.
8 Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke;
sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
9 Wanda yake ragwanci a aikinsa
ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
10 Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
11 Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga;
suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
12 Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,
amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
13 Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara,
wannan wauta ce da kuma abin kunya.
14 Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo,
amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
15 Zuciya mai la’akari kan nemi sani;
kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.
16 Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa
yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
17 Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya,
sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna.
18 Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa
ta kuma ajiye masu faɗan a rabe.
19 Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa,
kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.
20 Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika;
girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.
21 Harshe yana da ikon rai da mutuwa,
kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
22 Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau
ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
23 Matalauci kan yi roƙo da taushi,
amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.
24 Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,
amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.