21
Shigar mai nasara
(Markus 11.1-11; Luka 19.28-38; Yohanna 12.12-19)
Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”
Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,
“Ku ce wa Diyar Sihiyona,
‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,
mai tawali’u yana a kan jaki,
a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”* Zak 9.9
Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa,
“Hosanna Wani faɗi na Ibraniyanci mai ma’anar “Ceto!” Wanda ya kasance wani salon yabo; haka kuma a aya 15 ga Ɗan Dawuda!”
 
“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” Zab 118.26
 
“Hosanna a cikin sama!”
10 Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”
11 Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”
Yesu a haikali
(Markus 11.15-19; Luka 19.45-48; Yohanna 2.13-22)
12 Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. 13 Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’§ Ish 56.7amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”* Irm 7.11
14 Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. 15 Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.
16 Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?”
Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa,
“ ‘Daga leɓunan yara da jarirai
kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?” Zab 8.2
17 Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.
Itacen ɓaure ya yanƙwane
(Markus 11.12-14,20-24)
18 Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. 19 Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.
20 Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”
21 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru. 22  In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”
An tuhumi ikon Yesu
23 Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”
24 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. 25  Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?”
Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’ 26 In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”
27 Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”
Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”
Misalin ’ya’ya biyu maza
28  “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’
29  “Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.
30  “Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba.
31  “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?”
Suka amsa, “Na farin.”
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah. 32  Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
Misalin ’yan haya
(Markus 12.1-12; Luka 20.9-19)
33  “Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya. 34  Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi.
35  “Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun. 36  Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin. 37  A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’
38  “Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’ 39  Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.
40  “To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ’yan hayan nan?”
41 Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”
42 Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa,
“ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi
ne ya zama dutsen kusurwar gini.
Ubangiji ne ya aikata wannan,
kuma abin mamaki ne a idanunmu’? Zab 118.22,23
43  “Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani. 44  Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”§ Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da aya 44.
45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake. 46 Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.

*21:5 Zak 9.9

21:9 Wani faɗi na Ibraniyanci mai ma’anar “Ceto!” Wanda ya kasance wani salon yabo; haka kuma a aya 15

21:9 Zab 118.26

§21:13 Ish 56.7

*21:13 Irm 7.11

21:16 Zab 8.2

21:42 Zab 118.22,23

§21:44 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da aya 44.