8
1 Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye. 2 Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari. 3 Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu. 4 A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat. 5 Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana.
6 Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, 7 ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya. 8 Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa. 9 Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi. 10 Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi. 11 Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. 12 Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba.
13 A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe. 14 A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf.
15 Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, 16 “Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu. 17 Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.”
18 Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, 19 da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.
20 Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. 21 Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.
22 “Muddin duniya tana nan,
lokacin shuki da na girbi,
lokacin sanyi da na zafi,
lokacin damina da na rani,
dare da rana
ba za su daina ba.”