Ibraniyawa
1
1 A zamanin da, Allah ya yi wa kakanin kakanninmu magana ta hanyoyi ma su yawa iri iri, ta bakin annabawa. 2 Amma a zamanin nan na karshe, ya yi mana magana ta wurin Dansa, wanda ya sa magajin kome, wanda ta wurinsa ya halicci duniya. 3 Shi ne hasken daukakar Allah, ainihin kamanin zatinsa. Ya na rike da dukkan abubuwa ta ikon kalmarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a hannun dama na madaukaki a can sama. 4 Ta haka ya ke da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gada yake da fifiko nesa a kan nasu. 5 Domin kuwa wanene a cikin mala'iku Allah ya taba cewa, “Kai Da na ne, yau na zama Uba a gare ka?'' kuma, “Zan kasance Uba a gareshi, shi kuma, zai kasance Da a gare ni?'' 6 Kuma, da Allah ya kawo magaji a duniya, sai ya ce, “Dukan mala'ikun Allah su yi masa sujada.” 7 A game da mala'iku kuma sai ya ce, “yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, masu hidimarsa kuma harsunan wuta. 8 A game da Dan, ya ce “kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne. Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya. 9 Ka kaunaci aikin adalci, ka ki aikin sabo. Saboda haka Allah, wato Allahnka, ya shafe ka da man farin ciki fiye da tsararrakinka.” 10 “Tun farko, Ubangiji, kai ne ka hallici duniya. Sammai kuma aikin hannayenka ne. 11 Za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufafi. 12 Za ka nade su kamar mayafi, za su kuma sauya, amma kai kana nan ba sakewa, Har abada shekarunka ba za su kare ba.” 13 Amma wanene a cikin mala'ikun Allah ya taba cewa, “Zauna a hannun dama na, sai na sa makiyanka a karkashin kafafunka?'' 14 Ashe, ba dukkan mala'iku bane ruhohi, wadanda Allah yakan aika, don su yi wa wadanda za su gaji ceto hidima?