Nahum
1
Jawabi game da Ninebe a littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh.
 
Fushin Ubangiji a kan Ninebe
Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma.
Ubangiji Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma.
Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa,
yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa.
Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma.
Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba.
Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari,
gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa.
Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi;
yakan sa dukan koguna su kafe.
Bashan da Karmel sun yi yaushi
tohon Lebanon kuma ya koɗe.
Duwatsu suna rawan jiki a gabansa
tuddai kuma sun narke.
Duniya da dukan abin da yake cikinta
suna rawan jiki a gabansa.
Wa zai iya tsaya wa fushinsa?
Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa?
Ana zuba fushinsa kamar wuta;
aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa.
 
Ubangiji nagari ne,
mafaka kuma a lokacin wahala.
Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
amma da ambaliyar ruwa
zai kawo Ninebe ga ƙarshe;
zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu.
 
Dukan abin da suke ƙullawa game da Ubangiji* Ko kuwa Mene ne ku maƙiya kuke ƙullawa a kan Ubangiji? Shi zai kawo ga ƙarshe;
wahala ba za tă sāke komowa ƙaro na biyu ba.
10 Za su sarƙafe a ƙaya,
za su kuma bugu da ruwan inabinsu;
za a laƙume su kamar busasshiyar ciyawa. ma’anar kalman nan Ibraniyanci babu tabbas.
11 Daga cikinki, ya Ninebe wani ya fito
wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci
yana ba da mugayen shawarwari.
12 Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa,
za a yanke su, a kawar a su.
Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda,
ba zan ƙara ba ki azaba ba.
13 Yanzu zan karya karkiyarsu daga wuyanki
in kuma tsittsinke sarƙar da suka ɗaura ki.”
 
14  Ubangiji ya ba da umarni game da ke Ninebe,
“Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba.
Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera
gumakan da suke a cikin haikalin allolinku.
Zan shirya kabarinki,
domin ke muguwa ce.”
 
15 Duba, can a bisa duwatsu,
ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi,
wanda yake shelar salama!
Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda,
ki kuma cika wa’adodinki.
Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba;
domin za a hallaka su ƙaƙaf.

*1:9 Ko kuwa Mene ne ku maƙiya kuke ƙullawa a kan Ubangiji? Shi

1:10 ma’anar kalman nan Ibraniyanci babu tabbas.